💬
Home Politics Sports Wata motar haya da ta kwace, ta kutsa cikim masu bikin kirsimeti...

Wata motar haya da ta kwace, ta kutsa cikim masu bikin kirsimeti a jihar Gombe

Sponsored Advert
🔴 Breaking News:

An sami rudani a jihar Gombe a ranar Kirsimeti yayin da wani direban motar haya da ya kasa sarrafa motarsa ya buge wasu masu bikin Kirsimeti.

Sponsored Ad
Sponsored Ad

Newspot sun rawaito cewa masu bikin Kirsimeti din suna cikin wani jerin gwano daga unguwar Tumfure zuwa gidan gwamnatin jihar da fadar Sarkin Gombe don kai ziyara, lokacin da lamarin ya faru.

Mutane kimanin 22 daga cikin masu bikin Kirsimeti din sun jikkata a hatsarin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, da ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na tarayya dake Gombe da kuma Asibitin Kwararru don samun kulawa.

Sponsored

Sai dai, Abdullahi ya ce kawo yanzu babu wanda ya rasa ransa al’amarin.

Advertisement

Sponsored
Sponsored Ad - Ad Inserter Pro
Top Advert Bottom Advert

© Copyright © 2025 Newspot Nigeria. All rights reserved.
LAGOS WEATHER