💬
Home Politics Sports Babban ɗa ga gwamnan Jigawa ya rasu a hadarin mota

Babban ɗa ga gwamnan Jigawa ya rasu a hadarin mota

Sponsored Advert
🔴 Breaking News:

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya rasa dansa kwana guda kacal bayan rashin mahaifiyar sa.

Sponsored Ad
Sponsored Ad

Abdulwahab Umar Namadi ɗan fari ga Gwamna Umar Namadi ya rasu ne bayan wani haɗarin mota akan hanyarsu ta dawowa daga Kafin Hausa shi da abokansa, kwana guda da rasuwar kakarsa.

Abdulwahab mai shekara 24 shi kaɗai ya mutu cikin mutanen da haɗarin ya rutsa da su, yayin da aka garzaya da abokinsa asibiti domin kula da lafiyarsa.

Sakataren Labaran Gwamnan Hamisu Gumel ya tabbatar da faruqar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Alhamis.

Sponsored

An yi jana’izarsa a garin Kafin Hausa kamar yadda addini ya tanada.

Advertisement

Sponsored
Sponsored Ad - Ad Inserter Pro
Top Advert Bottom Advert

© Copyright © 2025 Newspot Nigeria. All rights reserved.
LAGOS WEATHER