Aƙalla mutane biyar ne akayi garkuwa da su a ranar Asabar a Obbo-Ayegunle, cikin ƙaramar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.
An sace mutanen ne yayin da suke dawowa Odo-Owa daga wajen bikin aure da aka gudanar a garin Ope, cikin Jihar Kogi mai makwabtaka, da misalin ƙarfe 4 na yamma.
Cikin waɗanda aka sace akwai Oloye Oyewole Abolarin, shugaban mafarauta na Odo-Owa, da matarsa, Funmilayo Abolarin, sai Tunde Oladipo da matarsa, da wata mace ɗaya Bose, duk mazauna Agbele Igbede a Odo-Owa.
Masu garkuwar sun tuntuɓi iyalan waɗanda aka sace, inda suka nemi fansar Naira miliyan 100 kafin su sake su.
Rahotanni sun nuna cewa iyalai da al’ummar gari sun fara tattara kuɗi domin cika buƙatar masu garkuwar. Sun kuma roƙi Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq da hukumomin tsaro da su kawo musu ɗauki.
Wani rahoton da ba a tabbatar ba ya nuna cewa an kuma samun sace sacen mutane a ranar Litinin a kan hanyar Omu-Aran.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Ejire Adeyemi Toun, ya ci tura, domin ba ta ɗauki waya ba kuma ba ta amsa saƙon da aka tura mata ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com