Za a buga wasan cin kofin duniya na 2034 a Saudiyya

Advertisement

An zabi kasar Saudiyya a matsayin kasar da za a gudanar da gasar cin kofin duniya ta shekarar 2034, yayin da Spain, Portugal da Morocco za su zama masu masaukin baki ga gasar ta 2030, kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA ta tabbatar.

Dukkanin kasashen da suka nemi daukar nauyin gasar sun kasance ba tare da ƙalubale ba kuma an amince da su a taron FIFA da aka gudanar ta yanar gizo a yau Laraba.

Saudi Arabia ce kadai ta nemi shiga gasar a shekarar da ta gabata cikin wani tsari mai sarkakiya wanda ya sa FIFA ta yanke shawarar hade zaben kasar da zata dau bakuncin gasra ta 2030 da ta 2034 a zama guda.

Wannan yana nufin cewa wakilan sun goyi bayan ko kuma suka ƙi goyon bayan duka tayin ɗaya ba tare da zaɓen rarrabe ba.

A taron, FIFA ta kuma amince da gasar cin kofin duniya ta 2030, wanda za a gudanar a ƙasashe guda shida a cikin nahiyoyi uku, inda za a fara wasanni uku a Argentina, Paraguay, da Uruguay

Advertisement

 

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com