Yayin da ya rage kwanaki 2 a shiga sabuwar shekara jihohi 28 basu amince da sabon kasafin kudi ba

Advertisement

Kawo yanzu gwamnatin tarayya da sauran jihohi 28, ciki har da Legas da Delta, na da kwanaki uku kacal su tabbatar da rattaba hannu kan kasafin kudinsu na shekarar 2025.

Newspot ta rawaito aƙalla jihohi takwas a Najeriya sun rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2025 kafin shiga sabuwar shekara.

Jihohin sun haɗa da Abia, Sokoto, Kaduna, Katsina, Anambra, Edo, Bauchi, da Enugu, inda gwamnonin jihohin suka sanya hannu kan dokar kasafin kudin a ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa Jihar Enugu ce ke da mafi girman kasafin kudi a matakin jihohi, wanda ya kai Naira biliyan 971. Sai Kaduna mai kasafin Naira biliyan 790, sannan Abia tana biye da Naira biliyan 750.2.

Sauran jihohin sun haɗa da Katsina (Naira biliyan 692.2), Edo (Naira biliyan 675), Anambra (Naira biliyan 606), Sokoto (Naira biliyan 526), da Bauchi (Naira biliyan 467).

Advertisement

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com