‘Yan sanda sun tabbatar da sace Fasto mai kula da Cocin Church of the Brethren in Nigeria, wanda aka fi sani da Ekklesiyar Yan’uwa A Nigeria (EYN), Rev. James Kwayang da sakatarensa, Rev. Ishaku Chiwar, a jihar Adamawa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da sace fastocin.
Nguroje ya bayyana cewa rundunar ta riga ta tura jami’anta domin ceto malaman biyu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
An sace Fastocin su a ranar Lahadi da misalin karfe 11 na dare a yankin karamar hukumar Song na jihar.
Shugaban EYN, Rev. Daniel Mbaya, wanda shi ma ya tabbatar da sace fastocin, ya yi kira ga jami’an tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa domin tabbatar da sakin malaman cikin koshin lafiya.
Ya kuma yi kira ga sauran shugabannin addini, dukkan cocin EYN, da daukacin ‘yan Najeriya su hada kai da cocin wajen yin addu’o’i sosai don samun ‘yancin malaman da aka sace.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com