Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta tarbi jaririn farko a shekarar 2025.
Ta fara ziyartar babban Asibitin Asokoro a Abuja, inda ta gabatar da kyaututtuka ga jariran farko namiji da mace da kuma sauran jarirai da aka haifa a ranar 1 ga Janairu.
Matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Nana Shettima da ta wakilci Rwmi Tinubu, ta bayyana cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa za ta ci gaba da ba da tallafi don tabbatar da kyakkyawan rayuwa ga yara a Najeriya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai a (Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa), Kwapchi Bata, ta fitar a ranar Laraba,.
Sanarwar ta ce:
“Favour Stephen Odion itace jaririya mace da aka fara haifa da misalin ƙarfe 12:27 na safiyar Laraba, 1 ga Janairu, 2025, mai nauyin 3.6kg. Haka nan, jaririn farko namiji na shekarar 2025, Zimchikachim Ejiofor, an haife shi da misalin ƙarfe 7:14 na safe, yana da nauyin 3kg.
A nata jawabin, Mukaddashiyar Babban Daraktan Asibitin Asokoro, Abuja, Dr. Rosemary Nwokorie, ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen sauya fasalin sashen lafiya don inganta ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya.
Ta kuma yaba da shirin Renewed Hope Initiative na Uwargidan Shugaban Ƙasa da matar Mataimakin Shugaban Ƙasa don tallafawa mata da yara masu rauni a Najeriya.”
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com