Tinubu, ka zama mai rikon amana – Limamin Legas

Advertisement

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Lekki, Lagos, Ridhwan Jamiu, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kasance mai rikon amana da adalci ga al’umma a koda yaushe.

Shugaba Tinubu ya halarci sallar Juma’a a Masallacin Juma’a na Lekki tare da sauran masu ibada ranar Juma’a.

Wannan sallar Juma’a ita ce fitowar Shugaban kasa ta farko a bainar jama’a bayan ya dakatar tarukan da aka sbirya yi saboda hadurrukan da suka faru a wasu sassan ƙasar.

Limamin ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu gode wa Allah a lokacin ni’ima da kuma haƙuri a lokacin jarabawa.

Limamin ya yi addu’o’i don samun nasarar Shugaban kasa wajen jagorantar Najeriya zuwa ga zaman lafiya, tsaro, da kuma ci gaba.

Advertisement

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com