Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sanar da naɗin Nwakuche Ndidi a matsayin shugaban riƙon hukumar kula da gidajen yarin ƙasar.
Sanarwar ta fito ne daga Ja’afaru Ahmed, sakataren ma’aikatar tsaron hukumar tsaro ta sibil difens, hukumar kashe gobara, da ta shige da fice, wanda ya bayyana cewa Ndidi zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Disamba.
Naɗin Ndidi ya zo ne bayan ƙarewar wa’adin Haliru Nababa, wanda ke rike da muƙamin yanzu.
Haliru Nababa ya sami naɗin shugaban hukumar ne tun a ranar 18 ga watan Fabrairu 2021, karkashin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Nwakuche Ndidi, wanda aka haifa a ranar 26 ga watan Nuwamba, shekarar 1966, a garin Oguta na jihar Imo, yana da kwarewa mai yawa a fannin gudanar da ayyukan hukumar.
Kafin wannan naɗin, ya kasance mataimakin shugaban hukumar mai kula da fannin horaswa.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com