Sanata Sumaila ya yaba wa Gwamna Yusuf kan nadin ɗan garinsu muƙamin kwamishina

Advertisement

Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, wanda ke wakiltar Mazabar Sanatan Kano ta Kudu, ya yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf kan nadin Nura Iro Ma’aji a matsayin kwamishina a majalisar zartarwarsa.

A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Sumaila ya ce nadin ya nuna sadaukarwar Ma’aji, kwarewa ta musamman, da hazakar da ya ke da ita.

Sanatan ya gode wa gwamnan bisa wannan karamci, ya ce tarihin ilimin Ma’aji da kuma gogewarsa a siyasa sun ba shi cikakkiyar damar da za ta ba da gudunmawa mai ma’ana ga jihar Kano.

Yana mai taya sabon kwamishinan murna, ya ce: “Ina da tabbaci cewa jagorancinka zai kawo manufofi da tsare-tsare da nufin magance kalubale da mu ke fuskanta tare kawo ci gaban Kano.

“A duk tsawon wa’adinka, ya zama wajibi ka gudanar da aikinka cikin himma, gaskiya, da kishi, yayin da ka kiyaye sunan danginka da martabar al’ummarka yayin da kake tafiyar da nauyin wannan sabon matsayi,” in ji shi.

Advertisement

Dan majalisar ya tabbatar wa Ma’aji da goyon bayansa wajen tabbatar da kyakkyawar alaƙa don ci gaban jihar Kano baki ɗaya.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com