Rundunar yan sanda ta bukaci Amnesty ta nemi afuwarta

Advertisement

Rundunar ‘Yan Sandan kasar nan ta musanta zarge-zargen da kungiyar kare hakkin dan’adam ta Amnesty International ta yi a rahotonta, inda ta bayyana shi a matsayin ƙarya, ds yaudara, da kuma kokarin bata sunan rundunar.

Rahoton, wanda aka wallafa a ranar 28 ga Nuwamba, 2024, ya zargi ‘yan sanda da kashe mutane ba bisa ka’ida ba yayin zanga-zangar, inda aka ce an kashe mutum 24 a jihohi shida na arewacin Najeriya.

Taboton mai taken “Bloody August: Nigeria Government’s Violent Crackdown on #EndBadGovernance Protests”, ya gamu da martani daga ‘yan sanda, waɗanda suka ce bincikensu ya saba da zarge-zargen Amnesty International.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa an kafa wata tawagar bincike ta musamman don tantance gaskiyar lamarin.

Ya bayyana cewa tawagar tare da haɗin gwiwar kwamishinonin ‘yan sanda daga jihohin da abin ya shafa sun gudanar da bincike mai zurfi tare da tattara rahoto da cikakken bayani da ke nuna kuskuren zarge-zargen Amnesty International.

Advertisement

“Mun shawarci Amnesty International suyi duba kan irin rahotannin ƙarya da suke yawan yi kan ayyukan jami’an tsaron Najeriya, su tabbatar da cewa rahotanninsu suna kunshe da gaskiya da adalci. Yin rahoto bisa gaskiya na da matuƙar muhimmanci ga mutuncin kowace ƙungiya ta duniya, “inji Adejobi.

Ya ƙara da cewa za su rubuta takardar neman janye rahoton daga Amnesty tare da neman afuwa ta fili kan zarge-zargen da suka yi ba tare da tushe ba.

“Rundunar ‘Yan Sandan tace za ta rubuta wa Amnesty International takarda don neman a janye wannan rahoto tare da neman afuwa. Rundunar ‘tace za ta ci gaba da kare haƙƙin kowa yayin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasa.

“Muna kira ga jama’a da su yi hattara da rahotannin da ke ƙoƙarin haifar da rashin amincewa da ƙarfafa rashin yarda da hukumomin tsaro,” inji Adejobi.

Yayin bayyana sakamakon binciken da aka yi a Borno, Adejobi ya ce ba gaskiya ba ne cewa ‘yan sanda sun yi amfani da bam kamar yadda rahoton ya yi iƙirari.

Ya ce, “A Jihar Borno, an tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun kasance masu tayar da hankali, suna wawure dukiya, lalata kadarorin jama’a. Alal misali, cibiyar koyon sana’o’in Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya an wawashe da kuma lalata ta.

“Gidan ajiya na World Food Programme da ke kan hanyar Baga/Maimalari Barracks, Maiduguri, shima an wawure shi, tare da lalata kayayyakin da ke ciki. Don haka, zargin Amnesty International cewa ‘yan sanda sun jefa bam daga wata mota cikin gidan mai ya kashe mutane uku ba gaskiya ba ne.”

A Jihar Neja, Adejobi ya ce zargin kashe mutum uku a Suleja bai tabbata ba a binciken da aka yi.

Haka kuma, Adejobi ya ce zargin batun kashe wani matashi mai shekara 21 a Katsina bai da tushe, inda ya ƙara da cewa majiyoyin cikin gida sun tabbatar da cewa ba a samu irin wannan lamarin ba.

Haka kuma, a Jihar Kaduna, Adejobi ya ce ba a samu zanga-zanga ba a ranar 1 ga Oktoba, 2024, kamar yadda Amnesty ta yi zargi, kuma babu wani kisa da ya faru a hannun ‘yan sanda.

Ya bayyana cewa an samu wani lamari da ya shafi Sojoji, wanda aka gudanar da bincike a kan sa a fili.

Adejobi ya ce Amnesty ta yi zargin kashe mata biyu da namiji ɗaya a Jigawa yayin zanga-zangar, amma binciken ‘yan sanda ya nuna babu wannan labari kuma hujjojin sun tabbatar da cewa mutum ɗaya da ya mutu ya rasa ransa ne sakamakon tashin hankali daga masu zanga-zanga ba a hannun ‘yan sanda ba.

A jihar Kano kuma, Adejobi ya ce rahoton ya yi zargin mutuwar mutane 12 a hannun ‘yan sanda, amma bincike ya nuna cewa sun mutu ne sakamakon rikici tsakanin masu kokarin satar kayan mutane da wasu bata-gari, amma ba a hannun ‘yan sanda ba.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com