NAFDAC ta lalata kayayyakin bogin naira biliyan 120 a watanni shida

Advertisement

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta sanar da cewa ta lalata kayayyakin bogi da suka kai kimanin Naira biliyan 120 da aka kama tsakanin Yuli da Disamba 2024 a fadin Najeriya.

Hukumar ta kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an dauki matakan da suka dace domin kare lafiyar su kafin, yayin, da kuma bayan hutun Kirsimeti.

Wannan bayani ya fito ne daga sakon taya murna na Kirsimeti da Darakta-Janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, wanda aka fitar a cikin wata sanarwa da Sayo Akintola, Mashawarci na kafafen yada labarai na hukumar, ya sanya hannu a ranar Lahadi.

Farfesa Adeyeye ta jaddada muhimmancin cin abinci mai lafiya a lokacin bukukuwan, inda ta ba da shawarar ga ‘yan Najeriya da su sayi abinci da abin sha daga wuraren da ke da adireshi da za a iya ganowa domin taimakawa hukumar wajen bin diddigin kayayyakin.

Farfesa Adeyeye ta sake jaddada kudurin NAFDAC na tabbatar da cewa kayayyakin abinci da magunguna masu lafiya da inganci ne za su kasance a kasuwar Najeriya.

Advertisement

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com