Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International tace akalla mutum 10,000 sun mutu a hannun sojojin Nijeriya tun bayan fara rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Da yake karin bayani kan wani rahoton kungiyar, a wani taron manema labarai, Daraktan kungiyar a Najeriya Isa Sunusi, ya ce sun je Maiduguri ne don tunatar da gwamnati game da bukatar adalci ga wadanda rayuwarsu ta lalace sakamakon rikicin Boko Haram da sojoji.
Sunusi ya jaddada cewa yaki da Boko Haram zai iya karewa nan ba da dadewa ba idan aka tabbatar da adalci.
Yace kungiyar ta shigar da kara a gaban Kotun Duniya dake Hague, tana zargin sojojin Nijeriya da laifin cin zarafin jama’a a Arewa maso Gabas.
Rahoton Amnesty din ya zargi sojoji da nuna kyamar duk wanda ya fito daga yankunan da Boko Haram ke iko da su, suna daukarsu a matsayin mambobin kungiyar.
Kungiyar tace tana da shaidun dake nuna sojoji sun aikata laifukan yaki, ciki har da hare haren da aka kai da gan gan, da kisan gilla, fyade da azabtar da wadanda basu ji basu gani ba.
Rikicin Boko Haram da sojoji a yankin dai ya mayar da hannun agago baya ta kowace fuska.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com