Majalisar dattijai ta yi sammacin ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo

Advertisement

Majalisar dattijai tayi sammacin ministan jiragen sama, Festus Keyamo da babban daraktan kula da sararin samaniya, Kyaftin Chris Njomo domin su ba da bahasi kan yadda harkar sufurin jiragen sama ta lalace a Najeriya.

An kuma yi sammacin wasu mamallaka kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kan yadda ake samun tsaiko ko kuma soke jadawalin tashin jiragen barkatai.

Sanata Abdulfatah Buhari daga jihar Oyo ne ya gabatar da kudirin, inda ya kalubalanci kwamitin ma’aikatar sufurin jiragen sama da lalubo hanyar kawo karshen wannan matsala.

Sanatan yace ya lura da yadda matsalar ke karuwa a yan kwanakin nan, inda yace “wannan abun damuwa ne matuka bisa la’akari da cewa jirgin sama shine hanya mafi sauki da sauri da yan kasuwa da kuma jami’an gwamnati wajen gabatar da ayyukansu cikin nutsuwa kuma akan lokaci.”

Ya kuma yi korafin cewa akwai karancin sa ido da tursasawa ga kamfanonin daga bangaren gwamnati.

Advertisement

Sanata Buhari ya ce sashi na 19 na dokar da ta kafa hukumar sufurin jiragen sama ta kasa ta tanadi kare Muradin fasinjoji, sai dai yawancin matafiya basu san suna da hakkin neman diyya kan bata lokaci ko kuma asara da kamfanonin jirage ke haddasa musu ba.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com