Kungiyar tsofaffin yan sanda ta yi barazanar yajin aikin cin abinci

Advertisement

Kungiyar tsofaffin ‘yan sandan Najeriya (NUP), reshen jihar Kano, ta yi barazanar fara yajin aikin cin abinci.

Kungiyar ta ce za ta dauki matakin ne domin matsawa gwamnatin tarayya da hukumar kula da fanshon ‘yan sanda su biya su hakkokinsu.

Sakataren kungiyar tsofaffin ‘yan sandan reshen jihar Kano, Kwamred SP Sa’idu Garba (rtd), ne ya tabbatar ne ya shaida wa manema labarai haka yammacin Laraba.

Ya ce dole ne su fara yajin aikin cin abincin saboda sun yi duk abinda ya dace a baya, ciki har da zanga-zangar lumana a majalisar tarayya domin neman a biya su hakkokinsu na giratuti.

Ya bayyana cewa fiye da shekara 10 suke bin hakkokinsu, amma har yanzu babu mafita.

Advertisement

Sai dai ya ce, a baya, zanga-zangar lumana da suka yi ta sa majalisar dattawa ta yi karatu na farko da na biyu kan kudirin cire su daga karkashin Hukumar Kula da Haraji ta Kasa (PenCom) wadda ke rike musu kudadensu.

SP Sa’idu Garba (rtd) ya ce abinda ake bashi a duk wata bai wuce N30,000 ba.

“Nayi ritaya daga aikin dan sanda tun shekarar 2007 tare da tarin iyali, amma abinda ake bani bai taka kara ya karya ba,” in ji tsohon dan sandan.

Ya ce dukanin shugabanninsu sun ki magana a kan abinda ya kira ‘zaluncin’ da ake musu’ saboda gudun rasa ayyukansu.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com