Kamfanonin sadarwa a Najeriya na iya samun izinin ƙara farashin kira, saƙonni da data a ƙarshen kwata na farko na shekarar 2025, a cewar wani babban jami’in ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa na ƙasar.
Babban jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) tana duba yiwuwar bai wa kamfanonin sadarwa izinin gyara farashi domin ya dace da yanayin tattalin arziki na yanzu.
Tun fiye da shekaru 11, kamfanonin sadarwa kamar MTN Nigeria, Airtel, da 9Mobile suna ta fafutukar neman a ba su damar gyara farashi domin su daidaita da hauhawar farashin gudanarwa. Duk da haka, ba a amince da karin farashi ba na tsawon wannan lokaci.
Masana harkar sadarwa sun bayyana cewa idan izinin ya tabbata, farashin ayyuka na iya tashi har zuwa kashi 40%. Wannan na nufin farashin kira na minti ɗaya zai iya ƙaruwa daga Naira 11 zuwa Naira 15.40, yayin da farashin saƙonni zai iya haura daga Naira 4 zuwa Naira 5.60. Sannan farashin data na 1GB zai iya ƙaruwa daga Naira 1,000 zuwa aƙalla Naira 1,400.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com