Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa nan bada jimawa ba za ta kaddamar da wani tsari na shekaru biyar mai kunshe da dabarun zuba jari a fannoni daban-daban domin jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na kasashen waje su shigo jihar.
Manufar wannan tsari ita ce kawo masu zuba jari don zuba jari a manyan sassan tattalin arzikin, wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar da samar da kudaden shiga ga gwamnati domin aiwatar da manyan ayyukan ci gaba.
Daraktan Janar na Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Kano (Kan-Invest), Muhammad Naziru Halliru, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Laraba.
A cewar Halliru, wannan tsari zai mayar da hankali kan gayyatar masu zuba jari don saka jari a bangarorin makamashi, noma, lafiya, ilimi, sufuri da sauran muhimman fannoni na tattalin arziki.
Ya bayyana cewa hukumar, tare da amincewar gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, za ta shirya bikin kaddamar da wannan tsari, wanda ya ce zai samar da yanayi mai kyau na kasuwanci don zuba jari ya samu bunkasuwa a jihar, wacce take cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya.
Haka zalika, ya ce hukumar za ta kaddamar da wani shiri na wayar da kai ga masu zuba jari na cikin gida domin su fahimci wuraren da za su zuba jari, “fiye da kawai gina manyan kantuna da shaguna.”
“A Kano kawai, muna da mutane masu arziki da za su iya zuba jari a fannin wutar lantarki wanda zai wadatar da jihar baki daya.
“Muna da masu kudi a Kano da za su iya zuba jari sosai a fannoni daban-daban na tattalin arziki. Wani lokacin ma, kawai mukan bukaci masu zuba jari na kasashen waje ne saboda fasaharsu ta zamani.
“Dalilin da yasa ba ma ganin su shi ne saboda gwamnati ta baya ba ta samar da yanayi mai kyau don zuba jari ba. Ba su ga tsarin doka da zai kare jarinsu ba. Ba su ga gwamnati tana ba su kulawa da muhimmancin da ake bukata ba, kuma ba ta samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ba, wanda hakan ya sa suke shakku wajen zuba jari,” inji shi.
Halliru ya sake jaddada kudirin hukumar na wayar da kan masu zuba jari na cikin gida don gano wuraren da za su zuba jari, “kuma ba kawai a gina manyan kantuna da shaguna ba.”
Ya ce gwamnatin jihar, ta hannun hukumar, tana aiki tukuru don samar da yanayin kasuwanci da ya dace da ka’idojin duniya, yana mai cewa za a kaddamar da wannan tsari cikin watanni kadan.
Haka kuma, Daraktan Janar ya bayyana cewa ajandar zuba jari ta gwamnan tana haifar da da mai ido, inda ya ce akwai shirye-shiryen zuba jari daga kamfanoni da dama domin zuba jari a Kano.
A cewarsa, mafi yawansu sun mika bukatar zuba jari a fannin samar da wutar lantarki ta hasken rana, yana mai bayyana cewa wasu daga cikinsu ma sun yi alkawarin zuba jarin da ya kai fiye da dala miliyan 500.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com