Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya dakata da shirinsa na gyare-gyaren haraji, yana mai cewa tsarin ba zai amfani arewacin Najeriya ba.
Mohammed ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis yayin taron bikin Kirsimeti da ya shirya wa al’ummar Kirista a jihar Bauchi.
A cewarsa, tsarin haraji da gwamnatin tarayya ke shirin aiwatarwa zai haifar da ƙalubale ga gwamnoni wajen biyan albashi da gudanar da ayyukan yau da kullum.
Ya ce: “Ƙudurorin haraji ba za su amfani yankin arewacin Najeriya ba. Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta saurare mu. Idan ba su saurare mu ba, hakan zai kai ga kama-karya, wanda ba shi da kyau.”
Gwamnan ya jaddada cewa bai kamata a samar da manufofi da za su fifita wata jiha kaɗai ba, yana mai cewa: “Ba batun addini ko ƙabilanci muke yi ba, magana ce ta haɗin kan ƙasa da tabbatar da adalci.”
Ya ƙara da cewa gwamnoni za su ci gaba da matsa lamba don ganin an ɗauki matakan da suka dace. “Idan kuwa suka ƙi, ba za su ƙi ganin martaninmu ba. Za mu tashi tsaye don yaƙar wannan lamari,” in ji shi.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com