Hukumar kididdiga ta Kasa (NBS) ta musanta cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta gayyaci shugaban hukumar, Adeniran Adeyemi, domin yin bayani.
NBS ta bayyana hakan ne bayan an yi kutse a shafinta na yanar gizo kuma aka saki wasu rahotanni kan biyan kudin fansa a Najeriya.
A ranar 17 ga Disamba, NBS ta fitar da rahoton binciken Crime Experience and Security Perception Survey. A cewar rahoton, ‘yan Najeriya sun biya jimillar Naira tiriliyan 2.23 a matsayin kudin fansa cikin shekara guda, daga Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024.
Bayan fitar da wannan rahoto, an samu rahoton cewa an yi kutse a shafin yanar gizon hukumar.
Daga nan sai jita-jita suka yadu cewa DSS ta gayyaci Adeyemi don tambayoyi kan yadda aka tattara bayanai da dabarun da aka yi amfani da su a rahoton.
Sai dai Kakakin NBS, Ichedi Sunday, ya musanta wadannan jita-jita, yana mai cewa DSS ba ta gayyaci Adeyemi ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sunday ya ce:
“Zan iya tabbatar da cewa rahoton ba gaskiya ba ne na kasance tare da shugaban hukumar kididdigar Kasa a daren jiya lokacin da wannan labari ya bulla, kuma babu wani kira daga DSS.
“Gidajen jaridu da dama sun tuntube ni, kuma na gaya musu cewa wannan labarin ba gaskiya ba ne. Na kuma yi magana da shi [Adeyemi] yau. don haka wannan ba gaskiya ba ne. Ban san dalilin da ya sa ake yada irin wannan bayani mara tushe ba.”
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com