Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima tare da wasu fitattun mutane sun hallara domin bikin daurin auren Ibrahim A. Bagudu, ɗan Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren, Atiku Bagudu, da Amina Tatari Ali, a Kaduna a ranar Juma’a.
Bikin ya gudana ne a masallacin Sultan Bello mai dimbin tarihi, inda manyan baki suka halarta, ciki har da gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris; gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum; da attajirin Afrika, Aliko Dangote.
Haka nan, hwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun; gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Ministan Tltsaro, Muhammad Badaru Abubakar; da Ministan kuɗi, Wale Edun, sun kasance a wajen taron.
Daurin auren ya samu jagorancin Bmbabban limamin masallacin Sultan Bello, Dr. Muhammad Suleiman Adam, wanda ya yi addu’o’in zaman lafiya da farin cikin ma’auratan.
A cikin wa’azinsa, limamin ya jaddada muhimmancin soyayya, haɗin kai, da imani wajen gina tushen iyali mai ƙarfi.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com