Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce kayayyakin da kasar nan ta shigo da su daga ƙasar Malta sun kusan na Naira biliyan 800 a watanni uku na ƙarshe shekarar 2024.Wannan adadi dai shi ne mafi girma da aka taba gani a tahirin ƙasar nan.
Alkaluman sun nuna saurin habakar bukatuwar kayyyakin Malta, wanda ya sa ta zama ƙasa ta biyar mafi girma da kasar nan ke shigo da kayayyaki daga garesu a wannan lokacin.
Kididdigar cinikayyar ta kai kashi 5.23 cikin 100 na jummalar kayayyakin da ake shigowa da su kasar nan, da ƙudinsu ya kai Naira tiriliyan 14 da biliyan 67.
Sai dai bincike ya nuna cewa babu bayanin shigo da wani kaya daga Malta a rubu’i na farko da na biyu na shekarar amma a rubu’i na uku, sai aka samu ƙaruwar shiga da kayayyakin daga ƙasar.
Duk da cewa rahoton bai tantance waɗanne irin kayayyaki aka shigo da su daga Malta ba, amma lamarin ya tayar da kura saboda zargin da Aliko Dangote ya yi a baya cewa ana shigo da man fetur daga ƙasar.
Dangote, ya kuma yi zargin kamfanin man fetur na kasa NNPCL nada matatar mai a Malta da ke kudancin Turai.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com