Shirin tallafawa tare da karfafa tattalin arzikinsu a jihar Kano (WEE) zai bada gudummawar kashi 30% na ci gaban tattalin arzikin jihar tare da fitar da mata sama da miliyan biyu daga kangin talauci.
Wannan ya fito ne daga bakin daraktar jukumar bincike da cigaba ta kasa dRPC, Dr. Judith Ann Walker, a yayin wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka gudanar a Kaduna.
Daraktan hulda da jama’a da sadarwa, Hassan karofi shine ya wakilci daraktar, inda ya bayyana manufar WEE a matsayin wani muhimmin shiri da zai kawo ci gaba mai dorewa a Jihar Kano.
Ta jaddada cewa wannan manufa tana da damar karfafa gudummawar tattalin arzikin mata da kuma taimakawa wajen samar da ci gaba mai dorewa.
Taron, wanda Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Kano ta shirya tare da hadin gwiwar DPRC da tallafin gidauniyar Ford, Africa Enterprise Challenge Fund, da WEE Catalyst Fund Partners, ya maida hankali kan kammala aiwatar da tsarin cigaban mata a jihar.
Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Kano, Hajiya Aisha Lawal Saji, wadda Alhaji Muntaka Iliyasu Yakasai, babban sakatare a ma’aikatar ya wakilta, ta sake tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na karfafawa mata.
Itama daraktar hukumar Isa Wali Empowerment Initiative, Hajiya Amina Hanga, ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da aiwatar da manufofin bayan samar dasu .
.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com