Kotu ta mayar da shugabannin kananan hukumomin Edo da aka dakatar

Advertisement

Wata babbar Kotun Jiha ta ba da umarnin dawo da Shugabannin Kananan Hukumomin Edo da aka dakatar.

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Efe Ikponmwonba, ta bayar da umarnin ne a ranar Juma’a, 20 ga Disamba, 2024.

Mai Shari’a Ikponmwonba ta yanke hukuncin ne kan karar da shugabannin kananan hukumomi 18 da ke cikin rikicin suka shigar tare da reshen Edo na Kungiyar Kananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON.

Wadanda ake kara sun hada da Gwamnatin Jihar Edo, da Gwamnan Edo da Mataimakin sa, sai Antoni Janar na jihar ds Akanta Janar

Alkalin ya amince da rokon masu karar tare da hana wadanda ake kara yin aiki da kudurin Majalisar Dokokin Jihar Edo na dakatar da masu karar.

Advertisement

Kotun ta kuma bayar da umarnin ci gaba da kasancewa a matsayin da ake a ranar 12 ga Disamba, 2024, har sai an saurari karar da aka shigar a ranar 12 ga Disamba, 2024.

Mai Shari’a ta dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga Fabrairu, 2025, don ci gaba da sauraro tare da bayar da umarnin aika sanarwar sauraro ga wadanda ake kara.

Jaridar Newspot ta ruwaito cewa Majalisar Dokokin Jihar Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 18 tare da mataimakansu bisa zargin rashin da’a da kuma saba doka.

’Yan majalisar sun dauki matakin ne biyo bayan wata takardar korafi da Gwamna Monday Okpebholo ya shigar kan shugabannin kananan hukumomin.

A cikin korafin, Okpebholo ya zargi shugabannin kananan hukumomin da rashin biyayya saboda gazawar su wajen gabatar da bayanan kudi na hukumomin su gareshi.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com