Kebbi: Gwamna Nasir Idris ya bude gasar karatun Al-Qur’ani na 39

Advertisement

Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya bude gasar karatun Al-Qur’ani ta kasa karo na 39 a dakin taro na Waziri Umaru Federal Polytechnic da ke Birnin Kebbi.

Jihar Kebbi ce ta dauki nauyin gudanar da wannan gagarumin taro, wanda manyan baki suka halarta, ciki har da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III; Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi; Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar; Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera; Sanata Abubakar Atiku Bagudu, tsohon Gwamnan Jihar Kebbi kuma Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare; Alhaji Saidu Nasamu Dakingari, tsohon Gwamnan Jihar Kebbi; da Alhaji Suleiman Muhammad Argungu, Sakataren Tsare-Tsare na Jam’iyyar APC ta Kasa, tare da sauran manyan baki daga sassan Najeriya.

A jawabinsa, Gwamna Idris ya nuna farin ciki da godiya kan damar da aka ba shi na daukar nauyin wannan gagarumin taro, musamman ganin cewa an yi sama da shekaru 20 ba a sake gudanar da gasar a Jihar Kebbi ba.

“Yau muna kafa tarihi. Ni ne mutum mafi farin ciki da aka ba damar daukar nauyin wannan muhimmin taron addinin Islama a Birnin Kebbi.

“Wannan dama ce mai ban mamaki, kuma lokacin da wakilai suka zo min da bukatar karbar bakuncin taron, ba ni da wani jinkiri wajen amincewa,” in ji shi.

Advertisement

Gwamnan ya kuma yi maraba da mahalarta gasar daga jihohi daban-daban tare da yaba wa wadanda su ka shirya taron bisa kyakkyawan aikin da suka yi don tabbatar da an yi nasara.

Shehun Borno, Mai Martaba Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, wanda ya kasance Uban Taron, ya jaddada mahimmanci da falalar Al-Qur’ani mai girma.

Ya yaba wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi kan jagorancinsa, ya kuma jinjinawa Gwamna Idris bisa karbar bakuncin taron.

Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, Farfesa Bashir Garba, wanda ya wakilci cibiyar shirya taron karkashin cibiyar nazarin addinin musulunci, ya bayyana Al-Qur’ani a matsayin jagora da albarka ga bil’adama.

Ya yi kira ga mahalarta da masu sauraro da su yi amfani da wannan dama don kusantar Al-Qur’ani da Ubangijinsu.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com