Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta bankado hadi da kwato kusan Naira miliyan 350 na kudaden ayyukan mazabun yan majalisar dokokin kasar.
Shugaban hukumar Dr Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana hakan a taron hukumar na ƙarshen shekara game da nasarorin da suka samu, inda ya ce hukumar ta hana zirarewar kuɗin gwamnati d ya kai naira biliyan 400 a 2024.
Hassan Salihu, mataimakin darakata a hukumar ta ICPC, ya ce sun bibiyi ayyukan mazaɓu 1,500 a jihohi 22 a faɗin kasar, inda a nan ne suka gano wannan badaƙala.
Yace ba’ayi aikin da aka tsara yi da wadannan kuɗaɗe ba, don haka suka kwato su.
Hassan Salihu, ya kara da cewa a duk shekara suna sanar da irin nasarorin da suka samu wajen yaki da cin hanci ”Mun bibiya ayyukan da kudinsu ya kai Naira biliyan dari shida da goma, sannan akwai kadarori da yawa da muka kama, sannan mun dakile yunkurin sace kudaden da aka so sacewa sun fi Naira biliyan talatin” a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa akwai wasu hukumomi da suka karrama bisa hadin kan da suke ba su, inda a wannan shekarar hukumar shirya jarrabawar Jamb da suka zo na daya, sai hukumar sufurin jirgin kasa da suka zo na biyu, da hukumar sayar da lantarki ta kasar da suka zo na uku.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com