Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa wajen magance matsalar karancin kudi da ake fuskanta a kasar.
Shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, yayi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu tare da Mista Emmanuel Ugboaja, Sakatare Janar na NLC, a ranar Alhamis a Abuja.
Sanarwar ta fito ne a karshen taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) da aka gudanar a Owerri.
A cewar Ajaero, NEC ta nuna damuwarta kan yadda karancin kudi ya ci gaba da zama babbar matsala, inda tace hakan yana kara jefa al’umma cikin matsalolin rayuwa.
Ya ce NEC ta lura cewa ‘yan Najeriya na tilastawa su sadaukar da kashi biyar cikin dari na kudaden su kowanne lokaci da suke tura kudi, wani hali da ba za a yarda da shi ba wanda ke kara tsananta matsalolin tattalin arziki da miliyoyin mutane ke fuskanta.
“Tasirin wannan ga kananan ‘yan kasuwa da sauran masu aiki a tattalin arzikin zamani yana da matukar girma, domin wannan yanayi na kara jefa talakawa da ma’aikata cikin babban kalubale,”
“NLC na neman gaggawar shigar gwamnatin don gyara wannan gazawar tsarin da kuma kare hakkin kudi na ‘yan kasa.
“Muna sa ran Gwamnan Babban Bankin Najeriya zai dauki matakai don tabbatar da cewa kudi suna samuwa ga jama’a don gudanar da harkokin kasuwancin su,” in ji shi.
Shugaban NLC ya kuma nemi a dakatar da kudirin haraji da ke gaban Majalisar Dokokin kasa domin samun tattaunawa da fahimtar juna mai ma’ana tare da ma’aikatan Najeriya.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com