Babbar kotun jihar Kano me Lamba 7 dake Sakatariyar Audu Bako, ta yankewa wani mutum hukuncin kisan ta hanyar rataya.
Alkaliyar Kotun mai sharia Amina Adamu ce ta yankewa Mutumin me suna Abba sulaiman hukuncin, a sakamakon samun sa da laifin hada kai da kuma kisan wani Tasi’u Ilyasu ta hanyar caka masa Wuka.
Tun a shekarar 2019 lamarin ya faru a unguwar Sauna Kawaji, biyo bayan wani rikici da ya barke a tsakani dangin wata Amarya da Uwar gidan ta, a sakamakon yadda aka yi zargin dangin Uwar gidan sun hana a shigar da Amaryar gidanta, lamarin da ya kaiga faruwar wancan kisa.
A yayin Shari’ar, me gabatar da kara Barista Usman Abdullahi Usman ya gabatar da shaidu guda biyu, inda lauyan wanda ake kara Barista Auwal Abubakar Ringim ya gabatar da wanda ake zargin kuma ya kare kansa.
Da take yanke hukuncin Mai sharia Amina Adamu tace ta gamsu da shedun da masu gabatar da kara suka gabatar mata, hakan ce ta sanya ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 5 a laifin farko na hada-kai, a inda laifin kisan kuma ta yanke masa hukunchin kisa ta hanyar rataya.
Bayan fitowa daga kotun, lauyan masu kara wanda kuma shine Lauyan gwamnatin Kano, Barista Usman Abdullahi Usman yace sun gamsu da hukuncin.
A nasa bangaren Lauyan wanda aka yankewa hukuncin Barista Auwal Abubakar Ringim, ya ce za su yi nazarin hukuncin domin daukar mataki na gaba
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com