Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aikewa da majalisar dokokin Kano wata wasika, wadda a cikin ta ya bukaci gwamnatin T’tarayya da ta aikowa da jihar Kano kasonta na rarar kudi daga tsarin iskar gas na Najeriya wato (NLNG) na tsawon shekaru 25 da suka gabata.
Da yake karanto wasikar, kakakin majalisar Jibril Isma’il Falgore, ya ce Gwamna Abba ya nemi majalisar ta shiga tsakani domin saukaka amso rarar kudin wanda hakkin jihar Kano ne tun daga watan Janairun 1999 zuwa yau.
A cikin wasikar, gwamnan ya ce, idan majalisar ta amince da kudurin, zai saukaka nemo maslaha don bin hanyoyin da suka da ce domin amso kudin da aka tara na tsawon shekarun, inda yace amso kudin, zai taimaka wajen kara karfin tattalin arzikin jihar nan tare da ba wa gwamnatin Kano damar magance muhimman abubuwan da ta sanya a gaba domin amfanin al’umma.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husseini Dala, ya jaddada cewa kudurin majalisar shine mabudin samun kudaden, yana mai bayyana cewa, hakan zai ba wa kungiyar gwamnoni damar daukar shawarwarin da suka dace domin amso kudaden zuwa jihohi.
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com