Shugaba Tinubu ya tabbatar da Najeriya zata zama jagora a fannin noma a 2025

Advertisement

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da Nijeriya ta zama jagora a fannin noma a cikin dukkan kasashen duniya nan da shekarar 2025.

Shugaban kasar ya bayyana hakan yayin jawabinsa a wurin taron kudu maso kudu na ajandar sake fata a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban ya kuma kaddamar da ayyukan samar da aikin noma, inda ya ce “Wannan aikin alama ce dake nuna cewa mun kuduri aniyar mayar da albarkatun da ba na man fetur ba kan gaba a yyukan mj don tabbatar da an wadata kasar”

Sabon shirin da aka kaddamar zai mayar da hankali ne kan sauya fasalin tattalin arziki ta hanyar noma isasshen abincin da za a iya ciyar da kasar a kuma fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje.

Advertisement

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com