💬
Home Politics Sports Shugaba Tinubu ya nada Ndidi sabon shugaban hukumar kula dagidajen yari

Shugaba Tinubu ya nada Ndidi sabon shugaban hukumar kula dagidajen yari

Sponsored Advert
🔴 Breaking News:

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sanar da naɗin Nwakuche Ndidi a matsayin shugaban riƙon hukumar kula da gidajen yarin ƙasar.

Sponsored Ad
Sponsored Ad

Sanarwar ta fito ne daga Ja’afaru Ahmed, sakataren ma’aikatar tsaron hukumar tsaro ta sibil difens, hukumar kashe gobara, da ta shige da fice, wanda ya bayyana cewa Ndidi zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Disamba.

Naɗin Ndidi ya zo ne bayan ƙarewar wa’adin Haliru Nababa, wanda ke rike da muƙamin yanzu.

Haliru Nababa ya sami naɗin shugaban hukumar ne tun a ranar 18 ga watan Fabrairu 2021, karkashin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Sponsored

Nwakuche Ndidi, wanda aka haifa a ranar 26 ga watan Nuwamba, shekarar 1966, a garin Oguta na jihar Imo, yana da kwarewa mai yawa a fannin gudanar da ayyukan hukumar.

Advertisement

Sponsored
Sponsored Ad - Ad Inserter Pro
Top Advert Bottom Advert

Kafin wannan naɗin, ya kasance mataimakin shugaban hukumar mai kula da fannin horaswa.

© Copyright © 2025 Newspot Nigeria. All rights reserved.
LAGOS WEATHER