💬
Home Politics Majalisa ta yi sammacin kwamishanan Nasarawa

Majalisa ta yi sammacin kwamishanan Nasarawa

Sponsored Advert
🔴 Breaking News:

Majalisar dokokin jihar Nasarawa tayi sammacin kwamishinan muhalli da albarkatun kasa, Yakubu Kwanta, domin ya bayyana a gaban majalisar a ranar Litinin, 16 ga Disamba, 2024, bisa tuhumar rashin biyayya.

Sponsored Ad
Sponsored Ad

Majalisar dai ta sha alwashin daukar tsatstsauran mataki kansa muddin ya gaza bayyana a gabanta.

Shugaban Majalisar, Danladi Jatau, ya bayar da wannan umarnin lokacin da shugaban kwamitin Majalisar kan Gidaje da Muhalli, wanda kuma ke wakiltar mazabar Keana, Muhammad Adamu Omadefu, ya gabatar da batun yayin zaman Majalisar a Lafiya, babban birnin jihar a jiya Alhamis.

Kwamishinan zai bayyana ne domin kare kasafin kudin ma’ikatar sa, a kasafin kudin 2025 da gwamnan ya gabatar.

Sponsored

Shugaba majalisar ya bayyana cewa ba za su lamunci kowanne irin rashin biyayya daga kowanne kwamishina a jihar ba.

Advertisement

Sponsored
Sponsored Ad - Ad Inserter Pro
Top Advert Bottom Advert

© Copyright © 2025 Newspot Nigeria. All rights reserved.
LAGOS WEATHER