Isra’ila ta shirya kai hari cibiyoyin makaman nukiliyar Iran

Advertisement

Rundunar Sojin Isra’ila ta kammala shirye-shirye domin kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, kamar yadda rahoton jaridar The Times ta Israel ta fitar.

Wannan matakin ya zo ne sakamakon canje-canjen siyasa a yankin, ciki har da matsalolin dake addabar kasar Iran da kuma faduwar mulkin Assad a Siriya.

Jami’an soja sun bayyana cewa yanayin ya samar da wata dama ta dabam ga Isra’ila domin tinkarar shirin nukiliyar Iran.

Rushewar mulkin Assad ya bai wa sojin saman Isra’ila damar lalata mafi yawan tsarin kariyar sararin saman Siriya, wanda a baya ya zama babban kalubale ga ayyukan sojin Isra’ila a yankin.

Rahoton ya kuma nuna damuwar da ke akwai cewa, Iran da ke kara fuskantar koma baya ka iya hanzarta shirinta na kera makaman nukiliya.

Advertisement

Yayin da karfin Iran a yankin ke kara raguwa, ana ganin za ta iya mai da hankali kan habaka shirinta na nukiliya, wanda ya sanya jami’an Isra’ila tunanin daukar matakan rigakafi.

Duk da cewa jami’an Isra’ila ba su tabbatar da wani shiri nan kusa ba, rahoton ya bayyana cewa komi na iya faruwa domin hana Iran mallakar makaman nukiliya.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com