Majalisar kolin harkokin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta sanar da naɗin sabbin limamai biyar da za su jagoranci babban masallacin kasa da ke Abuja.
An gabatar da sabbin limaman ne a taron da aka gudanar ranar Talata a Abuja, ta hannun sakataren janar na NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede.
Sabbin limaman da aka naɗa sun haɗa da Farfesa Ilyasu Usman (Jihar Enugu), Farfesa Luqman Zakariyah (Jihar Osun), Dr. Abdulkadir Salman (Jihar Kwara), Haroun Muhammad Eze (Jihar Enugu), da Farfesa Khalid Aliyu Abubakar (Jihar Filato).
Farfesa Oloyede ya bayyana cewa an yi naɗin ne bayan tantancewa da amincewa dukkanin kwamiticin da su ka dace.
Ya kuma ce tun daga kafa Masallacin Ƙasa a 1984, NSCIA tana zabar limamai masu cancanta don inganta ibada.
A jawabinsa, ya ce, “A madadin shugaban majalisar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ina mika sabbin limaman Masallacin Abuja ga jama’a, tare da addu’ar Allah ya albarkaci jagorancinsu da hikima da adalci wajen shugabantar al’umma.”
Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com