Gwamnatin Katsina za ta kashe N36bn a gina katafariyar hanya

Advertisement

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirinta na zuba jarin Naira biliyan 36.2 wajen gina wata hanya mai tsawon kilomita 54.7 da za ta haɗa Kadanya-Kunduru-Radda-Tsakatsa-Ganuwa, da ke tsakanin ƙananan hukumomin Charanchi da Kankia.

Ana sa ran kammala aikin cikin watanni 18, a cewar gwamna Mallam Dikko Umar Radda.

Da yake magana a fadar Sarkin Katsina yayin bikin ƙaddamar da aikin, gwamnan ya bayyana cewa kasafin kuɗin ya haɗa da ginin hanyar da kuma diyya ga masu gonaki da abin ya shafa.

Ya kuma bayyana cewa an riga an bayar da Naira biliyan 14, wato 40% na kuɗin aikin, ga kamfanin Stan Tech Engineering Construction Company domin fara aikin.

“Wannan hanya za ta zama wata mahada mai mahimmanci, wacce za ta taimaka wajen samun ilimi da kiwon lafiya, da kuma safarar kayan amfanin gona.

Advertisement

A nasa jawabin, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na jihar, Sani Ingawa, ya tabbatar da cewa hanyar za ta ratsa mazabu bakwai, ciki har da Kunduru a karamar hukumar Kankia.

A gefe guda, manajan daraktan Stan Tech Engineering, Mista Lee, ya gode wa gwamnati bisa damar da aka ba su, yana mai cewa an riga an fara share ƙasa da cika rairayi, duk da cewa an sami ɗan tsaiko sakamakon fitar da kayan amfanin gona daga gonaki.

An bayyana cewa aikin ginin hanya zai inganta tattalin arziki da cigaban zamantakewa a yankin.

Share your story or advertise with us: Whatsapp: +2347068606071 Email: info@newspotng.com